Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki 'Yan Kasar Filipino Biyar Da Aka Sace a Yankin Niger Deltan Najeriya


Jami‘an Gwamnati a Nigeria sun bada sanarwar cewa ma’aikatan man na ’yan ƙasar Filipinon da ’yan bindiga suka sace an sakosu a yankin Niger Delta.

Ma’aikatar harkokin wajen Philippines yau litinin ta tabbatar da labarin sakin ’yan ƙasarta biyar ba tare da ko ƙwarzane ba, kuma jami‘an jakadancin Philippine na kulawa dasu a birnin Tarayya Abuja.

Sai dai jami’in jakadancin Philippine dake magana dayawun ofishin jakadancin bai bada dalla-dallar ayanin abinda ya faru ba.

XS
SM
MD
LG