Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sa Ran Sabon Zababben Shugaban Kasar Amurka Barack Obama Zai Bayyana Sunayen Wasu Manyan Jami'an Gwamnatinsa Bada Jumawa Ba.


Wani lokaci a yau Alhamis zuwa gobe ne ake kyautata cewar shugaban Amurka mai jiran gado Barack Obama zai bayyana sunan sabon sakataren Baitul Malin Amurka, a dai dai lokacin da tattalin arzikin Amurka ke haɗuwa da tangarɗa, ana saura makonni goma kafin a rantsar da shi.

Yanzu haka shugaba Obama yana tattaunawa da manyan jami‘an hukumar ayyukan leƙen asiri waɗanda ke yi masa cikakken bayanin halin da ƙasa ke ciki ta fuskar tsaro da abinda ke faruwa a sauran madafun Gwamnatin Amurka.
Yayin da ake haka ne shugaba mai barin Gado George Bush a yau Alhamis ya tara dukkan ma‘aikatan fadar shugaban ƙasa ta White yayi masu jawabi cewar a mako mai zuwa zai tattauna da sabon shugaban ƙasa Barack Obama, snanan yayi masu godiya da haɗin kan da suka bashi tare da fatan zasu ci gaba da baiwa sabon shugaban cikakken haɗin kai.

XS
SM
MD
LG