Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Dauki Sabuwar Rantsuwa, Yace A Rufe Gidan Wakafin Guantanamo


Babban cif-jojin Amurka John Roberts ya sake rantsarada sabon shugaban Amurka Barack Obama bayan dan kuskuren da shi cif-jojin yayi a lokacinda yake rantsar da shugaban a karon farko shekaranjiya Talata.

A jiya da maraice ne Shugaba Obama ya sake daukan wannan rantsuwar a fadarsa ta White House, wanda bayansa ne ya tsunduma cikin aiki ka'in da na'in. A halin yanzu kuma mukarabban shugaban sunce a ya rattaba hannu akan dokar rufe gidan kurkukun nan na Guantanamo Bay dake a kasar Cuba, wanda Mr. Obama ke son ganin an dakile shi kwata-kwata nan cikin wa'adin shekara daya.

Wannan dokar ta nemi a kwashe dukkan mutane 250 dake kurkukun a kais u wani wuri. Haka kuma shugaban na son a sake nazarin dukkan laifukkan da ake zargin mutanen da aikatawa ta yadda za'a tantance wa'anda ya kamata a gurfanar a gaban shari'a. Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama, ciki harda ta Amnesty International, kamar su Geneve Mantari, sunyi marhabin da wannan matakin da sabon shugaban ya dauka.

Ko bayan wannan matakin, ana sa ran shugaba Obama zai bada wani umurnin da manufarsa shine ganin an kawo karshen azabar da wasu ma'aikatan tsaron Amurka kanyi anfani dasu akan mutanen dake tsare a wurinsu. Ta wani bangaren kuma, shugaba Barack Obama ya umurci kwamandojin sojan Amurka das u fara shata masa jadawalin janye sojojin Amurka dake Iraq.

Daman tun a lokacin da yake yakin neman zabe, Mr. Obama yayi alkawarin cewa, in ya zama shugaban kasa, zai janye dukkan sojan Amurka dake Iraq a cikin wa'addin wattani 16, yayinda kuma yake fatar kara yawan sojan Amurka din dake Afghanistan, inda ake samun Karin tashe-tashen hankulla a kwannakin nan.

XS
SM
MD
LG