Jami’an Najeriya sun ce sun yi odar maganin karya dafin gubar da aka yi amfani da
ita a hada maganin ciwon fitar hakori na yara,da tuni ya kashe jarirai 34. An sami karin mutuwar yara tara, kan 25 da
aka bada rahoton mutuwarsu cikin makon jiya,bayan an basu maganin mai suna “My
Pikin” “ko jariri na”.
Ana
baiwa yara maganin ne domin saukaka musu zafin tofin sabbinn hakora. Jami’ai
suka ce maimakon amfani da hade hade da aka saba,kamfanin mai cibiya a
Legas,sai ya yi amfani da wani hadi da ake amfani dashi wajen yin ruwan
lagirato da sauran ayyuka a manyan masana’antu.
Hukumar kula da lafiyar abinci
da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ce tana
sa ran samun kamar allurai dari na karya gubar daga Ingila. Hukumomi sun
ce ana janye maganin daga kasuwa,kuma an kama wadansu dangane da raba wan nan
magani.