Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pinochet Ya Mutu Ya Bar Baya Da Kura


Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam sunce za a tuna da Augusto Pinochet, musamman ta fuskar mulkin danniya da keta hakin dan adam da ya aiwatar a zamaninsa. Kamar yadda wani rahoto ya nuna, jami’an tsaron Chile a zamanin Pinochet, sun kashe fiye da mutum dubu uku da sukai adawa da gwamnatinsa bayan juyin mulkinsa na 1973.

Kimanin ‘yan kasar Chile dubu 30 ne suka bada shaidar an tsare su, aka kuma azabtar dasu a zamanin mulkinsa. Sebastian Bret, wani jami’in kungiyar Human Rights Watch, yace har yanzu Chile tana kokarin farfadowa daga bakin mulkin can na danniya.

“Har yanzu Chile tana kokarin warwarewa daga tarbiyyar mulki irin na danniya da Pinochet ya bar masu. A yayin da kasar ta sami ci gaba ta fannoni dabam dabam, har yanzu akwai matsaloli da dama dake bukatar warwarewa, kamar na fiye da mutun dubu da suka bace zamaninsa, kuma har yanzu ba a gano su ba.”

An haifi Augusto Pinochet a birnin valparaiso, rana 25 ga watan Nuwamban 1915. Ya kama aiki da rundunar sojin kasar, ya kuma rika samun daukaka, har zuwa shekarar 1973, lokacin da Shugaban Kasar dan gurguzu, Salvador Allende ya nada shi Hafsan Hafsoshin kasar. Wata uku da wannan nadi, tare da daurin gindin hukumar CIA ta Amurka, Janar Pinochet ya jagoranci hambare gwamnatin Shugaba Allende, ya kuma zazzage duk jami’an gwamnatin masu ra’ayin gurguzu.

Gwamnatin ta Soja ta kori majalisa, ta dakatar da harkokin siyasa, sa’annan kuma ta sanya wa kafofin yada labarai takunkumi. Janar Pinochet a wancan lokaci dai, ya kare wadannan bakaken manufofi a matsayin wani abu na lallai, don a hana ‘yan gurguzu kame madafun mulkin kasar.

Saidai Har yau, inji Sebastian Bret, akwai ‘yan kasar Chile da suka amince cewa zuwan Pinochet shine ya ceto kasarsu. Pinochet ya sauya manufar gurguzu da ya gada a Chile, ya rungumi Jari Hujja, ya kuma sayar da kadarorin gwamnati, sa’annan ya baiwa ‘yan kasuwa wani iko na fada a ji. Ian Vasquez, Daraktan Cibiyar Kyautata harkokin Kasuwanci ta Duniya, yace manufofin tattalin arzikin gwamnatin Pinochet, sune suka aza harsashin gina tattalin arzikin da Kasar ke tinkaho dashi a yau.

“Manufofin gwamnatinsa na tattalin arziki, sune suka sanya Chile ta tsere wa sa’o’inta na latin America, kuma sune suka sanya kasar a kan turbar ci gaba. Manufofinsa sunci nasara kwarai ta yadda har wadansu kasashen duniya, cikinsu har da irin su Amurka suka rika koyi dasu.”

Bayan ya tsallake wani yunkuri na hallaka shi a shekarar 1986, shugaban ya gudanar da wata kwarya-kwaryar kuri’ar jin ra’ayin jama’a, don ya gani ko zasu bashi damar wani zagayen shugabanci na shekara takwas, amma sai sakamakon ya nuna rashin amincewa.

Daga nan ne janar din ya rungumi kaddara, ya saki mukamin shugaban kasa, amma yaci gaba da rike shugabancin rundunar sojin kasar, daga baya kuma a shekarar 1998, ya zama dan majalirar Dattawa na rai da rai, mukamin da ya kare shi daga fuskantar tuhuma.

A watan Nuwamban shekara ta 2003, Janar Pinochet yai magana da wani dan jarida daga wani gidan talbijin na kasar Spain. Yace zuciyarsa a bude take, kuma baya nadamar komai na irin mulkin da ya aiwatar. Yace shi bai kashe kowa ba, bai kuma bada umarnin kashe wani ba. Wannan haramun ne, inji shi. Yace a fa tuna, shi kirista ne, kafin ya zama komai.a

XS
SM
MD
LG