Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Yayi Murdiya, Chavez Ya Sha Kaye


Nahiyar Turai ta bi sahun Amurka wajen kiran Rasha ta binciki koke koken jama’a dangane da wadansu aiyukan da suka sabawa akidar dimokradiyya a zaben da Jam’iyyar Shugaba Vladmir Putin ta lashe.

A halin yanzu da aka kusa kammala dukkan kuri’un da aka kada, Jam’iyyar Mr. Putin ta United Russia Party ta lashe kashi 64 bisa dari na zaben majalisar da aka gudanar Jiya Lahadi. Shugaban Hukumar Tabbatar da Tsaro da hadin Kan Turai, yace an ci zarafin wasu masu kada kuri’a lokacin zaben, musamman ma ‘yan adawa.

Sanarwa daga Ofishin Shugabar Jamus Angela Markel ma, tace babu gaskiya a zaben, babu kuma abin da ya hada shi da dimokradiyya.

A kasar Venezuela kuma, al’ummar kasar sun kada kuri’ar rashin amincewa da karawa shugaba Hugo Chavez karfi, ciki ko har da kyale shi yayi ta tsayawa takarar shugabancin kasar har illa ma sha Allahu.

Hukumar zaben kasar ta fada a yau cewa kashi 51 na masu kada kuri’ar sun ki amincewa da gyaran tsarin mulkin kasar.

Wannan ne karo na farko da Mr. Chavez ya sani nakasu a wajen masu kada kuri’a, tunda ya zama shugaban kasa, shekaru 9 da suka wuce.

A jawabinsa na karbar kaye, Shugaba Chavez yace sam wannan bai kashe masa jiki ba, kuma yanzu ma aka fara, a kokarinsa na tabbatar da mulkin gurguzu a kasar.

XS
SM
MD
LG