Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rice Da Gates Suna Ziyarar Gabas Ta Tsakiya


Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Condoleezza Rice da Sakataren Tsaro Robert Gates sun tattauna halin da ake ciki a Iraq, da sauran matsalolin Gabas ta Tsakiya da Sarki Abdullah na Saudi Arabiya, a Jeddah.

Gates yace Gwamnatin Shugaba Bush ta dauki Tsaron Yankin Gabas ta Tsakiya da Muhimmanci, dalilin da yasa ta tura dakarunta kasar Iraq, domin inganta tsaron gabas ta tsakiya. Tun da fari a wani taron koli da suka yi da kawayen Amurka a Sharm El Sheikh na Kasar Masar, jami’an Amurka sun yi kokarin tabbatarwa da kasashen larabawa cewa Amurka ta damu da su.

Rice tace tana fatan kyautata tattaunawa tsakanin falasdinawa da yahudawan Isra’ila.

XS
SM
MD
LG