Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigingimun Addini da Na Siyasa Suna Ci Gaba A Najeriya


Sojoji sunyi arangama da ‘yan bindigar nan da suka kashe sojoji goma sha uku a Birnin Knao, a bangare daya kuma jam’iyun adawa sunyi kira da a dake zaben shugaban kasa da za’ayi ranar Asabar mai zuwa.

Fadan na yau laraba ya biyo bayan harin da tsageru ‘yan gwagwarmayar suka kai kan ofishin yan sanda a kano jiya laraba, suka kashe yan sanda 12 da farar hula daya.

Cikin makon jiya an harbe kuma aka kashe wani shahararren malamin Islama, Sheikh Jafar Mahmud Adam, a wani masallaci cikin birnin.

A wani bangaren kuma, gaggan jam'iyun adawa kuma suna kira da a dage zaben shugaban kasa da za’ayi ranar Asabar, saboda dimbin magudin da suke zargin an tabka a zaben gwamnoni da majalisun dokokin Jihohi da aka gudanar a cikin makon jiya.

Gamayyar jamiyun adawa 18 sunce basu amince da sakamakon zaben na makon jiya da ya baiwa Jamiya mai mulki PDP gagarumin nasara ba. a

XS
SM
MD
LG