Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Chadi Ya Kara Tsamari- Yan Tawaye Na Kara Kusantar Ndjamena


Jami‘an Gwamnatin Chadi a birnin Ndjamena sun bayyana cewar basa zaton mayakan ’yan tawayen zasu iya kutsawa zuwa cikin birnin, amma duk da haka anga manya-manyan motocin yakin Gwamnatin Chadin na mirginawa zuwa muhimman wuraren birnin, tare da yiwa birnin kawanya kamar yadda aka ji wani dan jaridar kasar Chadi Adbangolo Mustaapha na fada.

Yace sojin Gwamnatin Chadi sun hana manema labarai kusantar gine-ginen Gwamnatin, kuma ana iya hangen mayakan ’yan tawaye jifa-jifa daga nesa, musamman a lardin Batha.

Anji wani jami’in ofishin jakadancin faransa yana cewa tun farko sun sami labarin cewa wata bataliyar mayakan ’yan tawayen ta fara dannowa zuwa babban birnin kasar Chadin, amma daga baya sai suka juya akalarsu zuwa wani bangaren.

Daga can bangaren gabashin Cahdin kuma sojin Gwamnatin Chadi sun sami nasarar sake kama birnin Abeche, birnin da mayakan ’yan tawayen Chadi karkashin laimar UFDD suka kama, kamar yadda aka ji jami’in ’yan tawayen na fadi.

Yace, mayakan ’yan tawaye sun ko riga sun fice daga birnin Abecehe ne domin zakudawa zuwa gaba jiya lahadi, sannan ’yan tawayen na son yin wasa ne da hankulan sojin Gwamnatin tare da basu tsoro kafin su afka masu. Yace dabara ce ta yakin sunkuru.

XS
SM
MD
LG