Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Shugabannin Pakistan Sun Dakatar Da Maganar Tsige Musharraf


Wanda ake sa ran zai zama Prime Ministan Pakistan, yace bashi da wani kuduri a halin yanzu, na tsige Shugaba Pervez Musharraf.

Amin Fahim, na jam’iyyar Mutanen Pakistan, ya gaya wa gidan talbijin na CNN cewa abin dake gaban sabuwar gwamnatin a halin yanzu, shine kammala mayar da kasar karkashin mulkin farar hula baki daya, kafin a fara tunanin makomar Shugaba Musharraf.

A da, manyan jam’iyyun hamayya guda biyu, PPP wadda ke karkashin jagorancin mijin marigayiya Benazir Bhutto, Asif Ali Zardari, da Jam’iyyar Islama ta Pakistan, wadda ke karkashin tshohon Prime Minista Nawaz Sharif, sun ci alwashin tsige shugaban, muddin da suka kaiga samun rinjaye a majalisa.

XS
SM
MD
LG