Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Fada Ya Barke A Yankin Darfur


‘Yan tawayen Darfur na kasar Sudan sunce sabon fada ya barke a wurare biyu, litinin dinnan.

Kakakin Kungiyar Tawaye ta JEM, yace dakarun gwamnati da jiraen yaki, sun kai hare-hare kan wuraren su, dake gabashi da yammacin Al-Fasher, babban birnin Arewacin Darfur.

An kuma ce an gwabza wani kazamin fadan a kudancin Darfur, kusa da Muhajiriya, wani gari da ‘yan tawayen ke rike da shi.

Majalisar Dinkin duniya ta baiyana damuwar ta da sake barkewar yakin a kusa da El-Fasher, garin da yawancin dakarun kiyaye zaman lafiya na Afirka da na Majalisar suke.

XS
SM
MD
LG