Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joe Biden, Sarah Palin,Zasu kara a St Louis A Daren Alhamis Din Nan


A St.Louis Missouri,dan Majalisar Dattijan Amurka, Democrat Joe Biden,da Gwmamnan Alaska,Republican Sarah Palin, zasu kara a daren Alhamis din nan,a muhawara daya rak tsakanin masu takarar mataimakan shugaban kasa.

Ana sa ran matsalar Tattalin Arziki zata zame babban batu a muhawarar da za a yi a St. Louis,Missouri,kuma za a maida hankali ainun kan Palin, wacce kusan bakuwa ce a sisayar kasa.

Daukar Sarah Palin a matsayin mataimakiyar shugaban kasa, da dan takarar shugabancin Amurka John Mccain na Republican yayi, ya tsuma magoya bayan Jam’iyyar masu ra’ayin rikau,amma masu suka suna shakkar ko tana da kawarewar zama mataimakiyar shugaban kasa. Mccain a hira da yayi da tashar talabijin na CNN,ya kare Sarah palin,kuma yace yana da kwarin gwiwa kan kwarewa da shugabancin ta.

Palin zata kara da tsohon hanu a Washington, Senator Joe Biden,daga Deleware,wadda matsalar sa itace tabka kura kurai.

XS
SM
MD
LG