Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Condoleeza Rice Tana Ganawa Da Jamian Israila Da Falasdinu A Kokarin Matsawa Sassan Biyu Duka Su Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya


A yau litinin, Sakatariyar harkokin Wajen Amurka Condoleeza Rice, take ganawa da Jami’an Isra’ila da Falasdinu,a kokarin karshe kamin ta bar yankin na samun a cimma yarjejeniyar kara samun zaman lafiya a ziyarar baya bayan nan da ta kai birnin kudus.

Tunda farko a yau litinin,Rice ta gana da wakilai a teburin shawarwari daga sassan duka biyu,tsohon PM Ahmed Qureia, da Ministan harkokin wajen Isra’ilaTzipi Livini. Bayan a jiya ta gana da Ministan Tsaron Isra’ila Ehud Barak, da Frime Ministan Yankin Falasdinu Salam Fayyad ,Rice ta sami tabbaci daga Isra’ila cewa zata sassauta tarnaki da ta azawa Falasdinawa a yammacin Kogin Jordan.

Isra’ila ta bada sanarwar cewa zata cire kananan shingaye hamsin,da wani babban wurin binciken ababan hawa dake dabaibaye zirga zirga cikin manyan biranen dake yammacin kogin Jordan. Jami’an Falasdinu kuma sunyi alkawarin inganta tsaro a Jenin,koda shike Isra’ila zata ci gaba da dawainiyar iko.

Daga bisani litinin din nan, Rice zata yi tattaki zuwa Amman,babban birnin Jordan,domin tattaunawa da shugaban yankin falasdinu Mahmoud Abbas, kamin ta bar yankin.

XS
SM
MD
LG