Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarcozy A Nijar - Tandja Yace Babu Tazarce


Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa yace dole ayi adalaci a cudanyar cinikayya da ake a tsakanin kasashen Afrika da na Turai.

Da yake magana a birnin Yamai na Junhuriyar Nijer a karshen rangadin kwannaki biyu day a kai zuwa kasashen Afrika guda ukku, shugaban na Faransa yace ba yadda harakar zuba jari zata yi alfanu idan ba kowane bangare na samun alherin day a cancance shi ba.

A kwanan baya ne dai kamfanin hakar ma'dinin uranium na Faransa, Areva, ya kulla wani shiri da ita gwamnatin Junhuriyar Nijer na soma hakar uranium din dake a yankin Anou Araren dake arewancin kasar kuma mai arzikin uranium, duk kuwa da tashe-tashen hankullan da 'yan tawayen Azbinawa ke haifarwa a wurin.

A wani labarin, Shugaba Tandja Mamadou na Jamhuriyar Nijar din yace ba zai yi kokarin sauya tsarin mulkin kasar domin zarcewa da mulki ba. Yayi wannan alkawari ne a wajen wani taron manema labarai da suka gudanar tare da Shugaban Faransa Nicolas Sarcozy.

Yace tarbiyyarsa ta soja, ba zata kyale shi ya karya doka ba, don saboda kawai ya ci gaba da mulkar kasar, wadda ya shekara goma yana jagoranta. Saidai yayi wani kandagarki, inda yace idan al'ummar kasar Nijar suka bukaci ya zarce, duk da wannan kuduri nasa, to a guje zai karbi goron gayyata su.

An dau dogon lokaci dai, tsakanin masu kaunar tazarcen Shugaba Mamamadou Tandja, da wadanda ke adawa da shirin, inda masu son ci gaba da mulkin Tandjan suke cewa suna so ya ci gaba da aiyukan alherin da ya fara. Su kuma masu adawa da zarcewar tasa, suna cewa tunda dai ba gado bane, kuma ba shi kadai Allah ya baiwa hikimar mulki ba, to ya ja da baya, wani kuma ya shigo ya gwada irin tasa basirar.

XS
SM
MD
LG