Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar Ya Ziyarci VOA


Shugaban Sashen Hausa Sunday Dare da Aliyu Mustafan Sokoto sune suka tarbo Sarkin daga bakin kofa, daga nan kuma suka zarce kai tsaye zuwa Sashen Africa Inda Daraktan Muryar Amurka Dan Austin da Shugabar Sashen Africa, Gwandolyn F. Dillard tare da Mataimakinta Ngussie Mangessa suka karbe shi.

A Jawabin da suka yi masa na maraba, Shugabannin sun shaidawa Sarkin cewa Muryar Amurka ta kammala shirye shiryen fito da wani sabon shiri a kan Addinin Musulunci mai suna ‘Musulunci Kenan’ ko kuma Islam In Action, domin a kara fadakar da al’ummar duniya kan Addinin Musulunci.

Suka ce wannan ya zama wajibi ganin yadda al’ummar duniya suke da kishirwar sanin hakikanin yadda addinin musulunci yake, da kuma bukatar a kawar da wadansu nau’o’i na rashin fahimtar addinin musuluncin a aikace. Sarkin Musulmin yayi murna da jin wannan labari, ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmawarsa domin tabbatar da nasarar wannan sabon shiri.

Sarkin ya kai ziyara ta musamman ga Sashen Hausa, inda ya gaisa da ma’aikata, ya kuma baiyana farin cikinsa da yadda suke kokarin fadakar da al’umma, musamman ma na gida. Ya bukacesu da su sanya kishin kasa a lokacin da suke gudanar da aiyukansu.

Daga baya sarkin yayi hira da sashen Hausa, ya kuma yi ta turanci da sashen Talbijin. Wadanda suka rako Sarkin sun hada da Magajin Rafin Sokoto, Alhaji Rilwan Bello, da Sarkin Kudu, Alhaji Mu’azu Bello da Kogunan Sokoto, Alhaji Nasiru Danladi Bako, da Mataimakin Shugaban Jami’ar Usman dan Fodio ta Sokoto, Farfesa Tijjani bande. Sauran sun hada da Dr. Hamid Bobboyi, da Alhaji Ahmed dasuki, da Kwamishinan Tattalin Arziki na Jihar Sokoto, Alhaji Kabiru Aminu Tafida, da Alhaji Sardauna Habib.

XS
SM
MD
LG