Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Kudi Na Najeriya Yace Saboda Faduwar Farashin Mai,Kasar Zata Sake Lalen Kasafin Kudin Shekara Mai Zuwa


Ministan kuɗin Nigeria Shamsudeen Usman yace faɗuwar da farashin mai keyi a kasuwa yasa ala tilas a rage yawan kuɗin da za’a kashe a kasafin kuɗin shekara mai zuwa.

Dr. Shamsudeen Usman yau Juma’a a birnin Tarayya na Abuja yake shaidawa manema labarai cewa bashi da zaɓin da ya wuce rage kuɗin kasafin a kowane ɓangaren da Gwamnatin ke gudanar daayyukanta. Daman dai tattalin arzikin Nigeria ya ta‘allaka ne a kan man da atake saidawa ƙasar waje, domin a kan farashin ne Nigeria ake tsara kasafinta kowace shekara.

A halin da ake ciki, Ma’aikatar lafiyar Nigeria ta bada sanarwar samun nasarar daƙile bazuwar ciwon amai da gudawa-Cholera- sanarwar ma’aikatar tace jihohi biyar sun tagaiyara sosai kafin cin ɗungumin cutar. Babban Darekta a ma‘aikatar lafiya Dr. Abdul Nasidi yayi ƙarin haske kan matakan da aka ɗauka kafin a kai ga samun nasarar. Dr. Nasidi yace haƙiƙa jami‘an lafiya sun tabbatar da ɓullar cutar Cholera a wasu majalisun kananan Hukumomi.

XS
SM
MD
LG