Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Gabatar Da Jawabin Karshe Ga Majalisa


A Karo na bakwai, kuma na karshe, Shugaba George W. Bush na Amurka ya halarci zauren Majalisar Wakilan Kasar, inda ya gabatar da jawabinsa na bakwai, kuma na karshe a cikin mulkinsa, kan halin da kasa take ciki.'Yan Majalisa sunyi layi a harabar Majalisar, inda suka tarbe shi, ga kuma gidajen talbijin na kasashen duniya suna nuna abin dake faruwa kai tsaye.

Bai fito kai tsaye yayi maganar tsawon shekaru bakwai na mulkinsa ba, amma dai yayi gugar zana kan manufofin gwamnatinsa, inda ya fara da karin sojojin Amurka dubu talatin da gwamnatinsa tayi a a a Iraq, wanda aka yi ta takaddama a kai. Yace Wadansu zasu iya cewa wannan kari baiyi wata rana ba, amma su kansu 'yan Alkaida, a halin yanzu hanyar gudu suke nema daga Iraq.

Kusan rabin jawabin nasa duk yafi bada fifiko ne ga manufar gwamnatinsa ta dangantaka da kasashen duniya, musamman ma a Gabas ta Tsakiya. Shugaba Bush ya baiyana fatansa na ganin cewa kokarin sulhu tsakanin Falasdinawa da Yahudawa ya cimma nasara.

Ya kuma aike da sakon kalubale ga gwamnatin Iran, inda yake cewa ku fito fili ku fadi gaskiyar niyyarku ta kera makaman nukiliya, ku daina gallazawa mutanenku a cikin gida, kuma ku dakatar da goyon bayan ta'addanci da kuke yi a kasashen duniya. Amma dai ina so ku san cewa, Amurka zata tunkari duk wanda ya kalubalanci sojojinmu, zamu goyi bayan kawayenmu, kuma zamu kare muhimman bukatunmu a yankin Gulf.

Mr. Bush ya kuma yi maganar kokarin gwamnatinsa na kare tattalin arzikin Amurka. Yace ya fahimci damuwar Amurkawa cewa cacar bakin dake tsakanin gwamnati da majalsa, zata iya shafar tattalin arziki, ya kuma yi kokarin kwantar masu da hankula.

Yace a karshe dai, Ina baiwa Amurkawa tabbacin cewa tattalin arzikinmu zai bunkasa, amma wannan bunkasa zata dauki lokaci, saboda a yanzu, sannu a hankali abin zai rika tafiya.

Daga karshe dai, Shugaba Bush ya shawarci Amurkawa da su ajiye siyasa a gefe guda, musamman a wannan lokaci da ake tafka muhawara mai zafi, tsakanin masu neman zama shugaban kasa na gaba.

XS
SM
MD
LG