Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yace Amurka Tana Samun Nasara A Iraki


A yau laraba shugaba Bush na Amurka yayiwa kasa jawabin tunawa da cika shekaru biya da shigar sojin Amurka Iraqi, sannan kuma ya kare manufofin Gwamnatinsa game da dalilan hambaras da Gwamnatin Saddam Hussain tare da gargadin matsalar da za’a shiga idan har Amurka tayi saurin janyewa daga Iraqi.

Wani jawabin da ya yiwa jami‘an tsaro a ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon dazu da hantsi, shugaba Bush yace ya zuwa yanzu dai Amurka na samun nasara a kutsen da sojinta keyi a Iraqi musamman bayan karin sojin da aka tura dubu Talatin domin wargaza tarzomar ’yan shi’a.

Yace sojin Amurka sun kuma sami nasarar lalata sansanonmin al-qaida a Iraqi da cin lagon karfin akidar Osama bin Laden.

Kazalika suma ’yan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Democrat Hillary Clinton da Barack Obama kowanensu yayi yiwa kasa jawabi game da manufofinsu a Iraqi.

XS
SM
MD
LG