Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Hugo Chavez Ya Sake Lashe Zaben Venezuela


Bayan ya sake lashe zaben shugabancin Kasarsa na wani sabon wa’adin shekaru shidda, shugaba Hugo Chavez na Venezuela yace zai ware kaso mafi tsoka na arzikin man kasar don hidimtawa matalauta.

Ranar Litinin din nan Mr Chavez yayi bikin nasarar da ya samu a Caracas, bayan ya sami galaba a zaben da aka gudanar jiya lahadi. Shugaba Chavez ya ja hankalin masu kada kuri’a ne da kalamansa na ci gaba da salon mulki irin na gurguzu, da kuma tsananin adawarsa da Amurka.

A jawabin da ya yiwa jama’ar kasar bayan an tabbatar da nasararsa, a gaban dubban mutanen da suka yi tururuwa domin nuna goyon bayansu da maraicen Lahadi, Mr Chavez yace zai fara wani sabon salon abinda ya kira juyin juyi halin Boliver. Shirin dai ya samo asalinsa ne daga sunan jagoran gwagwarmayar neman ’yanci a karni na goma sha tara, Simon Boliver, kuma an bullo da shi ne domin tallafawa marasa galihu.

Mr Chavez yace nasararsa, alama ce ta shan kaye ga shugaba Bush, mutumin da Sugaba Chavez ya kira iblishin dake neman mamaye duniya.

Abokin hamayyar Mr Chavez, gwamnan jihar Zulia, Manuel Rosales ya rungumi kaddara bayan jagorantar kalubale mafi tsanani da shugaban Chavez ya taba fuskanta cikin shekaru da dama.

XS
SM
MD
LG