Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba ‘Yar Aduwa Ya Rungumi AFRICOM


Shugaba Umar Musa ‘Yar Aduwa, yace kasarsa zata hada guiwa da sabuwar rundunar AFRICOM, dake karkashin kulawar sojojin Amurka.

A jiya Alhamis Shugaba ‘Yar Aduwa da Shugaba Bush suka gudanar da wani taron manema labarai, bayan kammala wata ganawa da sukja yi a fadar White House.

Shugaban na najeriya yace shi da Shugaba Bush sun tattauna al’amuran da suka shafi tsaro a Afirka, ciki kuwa har da halin da ake ciki a yankin Niger Delta da mashigin Guinea. Yace Najeriya zata hada kai da AFRICOM wajen tabbatar da zaman lafiya, ba ma a Africa kawai ba, har da sauran sassan Afirka.

Ba a bayar da cikakken bayani kan yadda wannan hadin kai zai kasance ba tukuna. Da dai, Shugaba ‘Yar Aduwa ya taba cewa ba zai bari ayi amfani da Najeriya wajen girke dakarun na AFRICOM ba, ba kuma zai goyi bayan girke su a ko wacce kasar Afirka ta Yamma ba.

Da yammacin jiya Alhamis Shugaban Kasar na najeriya ya jagoranci taron ‘yan kasuwar Amurka da takwarorinsu na Najeriya. Da yamma kuma aka yi masa liyafa a Ofishin Jakadancin Najeriya a Amurka dake birnin Washington.

XS
SM
MD
LG