Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Somaliya Yayi Murabus


Shugaba Abdullahi Yusuf Ahmed na Somalia ya fada a yau Litinin cewa zai sauka daga kan mukamin sa, inda shugaban Majalisar kasar zai maye gurbinsa kafin a zabi sabon shugaba.

Shugaba Abdullahi Yusuf ya amince cewa gwamnatinsa, wacce ke da goyon bayan majalisar Dinkin Duniya, bata da wani katabus in banda a cikin biranen Mogadishu da Baidoa, inda mazaunin Majalisar yake.

Kwanan nan gwamnatin ta cimma wata yarjejeniya da wata kungiyar masu sassaucin kishin Islama, ARLS, amma kungiyoyi masu matsanancin ra’ayi suka yi watsi da wannan yarjejeniya, suka kuma ci gaba da mamaye yankunan kudu da tsakiyar kasar.

Fada tsdakanin kungiyoyin sa kai, da gwamnatin wacce dakarun kasar Habashe ke mara wa baya, yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a Somaliya, miliyoyin kuma suka rasa matsugunansu.

XS
SM
MD
LG