Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Yahudawa Da Na Falasdinawa Sun Fara Tattaunawa


Jami’an Isra’ila sunce ba a kaiga tattauna matakin karshe na kafuwar kasar Falasdinawa ba tukuna, kamar shata kan iyakokin kasasshen biyu, rushe gidajen Yahudawa ‘yan kaka-gida a yankin Yamma da Kogin Jordan, da kuma makomar Birnin Kudus.

Mr. Olmert yayi tattaki zuwa garin Yamma da Kogin Jordan na Jericho, ziyara irinta ta farko da wani Prime Ministan yahudawa ya taba kaiwa wani garin Falasdinawa cikin shekaru bakwai.

Ziyarar tana da nasaba da shirye shiryen da ake yi na gudanar da wani babban taron koli kan zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Wakilin Falasdinawa Sa’eb Erekat yace akwai bukatar ci gaba da tuntubar juna domin kintsawa taron sosai.

A shekarar 1967 Isra’ila ta kwace yankin Yamma da Kogin Jordan, a yakin Isra’ila da kasashen larabawa. A yau yankin ya zama wani hadin gambizar gidajen yahudawa ‘yan kaka-gida, da yankunan dake karkashin mulkin Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG