Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Habasha Sun Doshi Kismao


Shaidun gani da ido a kudancin Kismao sunce dubban mayakan masu kishin Islama sun saje da jama’a yau Litinin, bayan mayan bidigogin atilare na Habasha sun mirgina cikin garin Jilib, kilomita 45 arewa da Kismao a jiya. Manyan jagororin masu kishin Islaman, irin su Sheikh Hassan Dahir Aweys, sunyi tunga a garin na Jilib, bayan sojojin Habasha sun kame birnin Mogadishu ranar Alhamis.

Wani dan Jaridar Smaliya dake zaune a Kismayo, Nafteh Dahir Farah, ya gaya wa Muryar Amurka cewa garin ya shiga cikin rudu, a inda ‘yan bidiga suka rika bin tituna suna kwasar makamai daga rumbunan makamai da masu kishin Islaman suka bari.

A ‘yan makonnin da suka gabata dai, fiye da rabin Somalia tana hannun masu Kishin Islaman, wadanda suka kora gwamnatin rikon kwarya mara tagomashi a cikin gida, wadda ke da goyon bayan manyan kasashen duniya zuwa garin Baidoa. Sun dai ce so suke so su dawo da bin doka da oda a Somalia, wadda ta rasa wani tartibin jagora har na tsawon shekaru 15, ta hanyar kafa mulki irin na Islama.

Amma Makwabciyarsu Habasha da daurin gindin Amurka, ta zargi masu kishin Islaman da niyyar kafa wani sansanin Al-Kaida a Gabashin Africa da kawo rashin zaman lafiya a yankin gaba daya, tare da goyon bayan babbar abokiyar gabar Habasha, wato Eritrea.

Kimanin Kwanaki goma da suka wuce, Habasha, tare da goyon bayan Amurka, ta shiga cikin rigimar, inda ta baiwa mariliyar gwamnatin rikon kwaryar goyon baya, suka kuma kai ga wargaza rundunar masu kishin Islaman.

Dan jarida Nafteh Hassan farah, yace an ga manyan jagororin masu kishin Islaman guda biyu, Sheikh Hassan dahir Aweys da Sheikh Sharif Sheikh Ahmed suna barin Kismayo da sanyin safiyar Litinin dinnan, sun doshi kan iyakar Kenya, kimanin Kilimita 160 daga kudancin Somaliya. Aweys dai yana cikin mutanen da Amurka tace tana nema ruwa a jallo, saboda zargin aiyukan ta’addanci. A kusa da kan iyakar da suka dosa dai, akwai wani sansanin masu kishin Islaman dake, kauyen Ras Kamboni, inda suke horas da mayakansu.

Shugabannin masu kishin Islaman dai sunce ja da baya ga rago, ba tsoro bane, shirin yaki ne. Sun kuma ce zasu fara kai zafafan hare-haren sari ka noke, ko na kunar bakin wake irin wanda ake fama dashi a Iraqi a halin yanzu, kan Habasha da gwamnatin Somaliya ta rikon kwarya.

XS
SM
MD
LG