Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Taron Dangi A Afghanistan Sunce Sun Raunana Mayakan Sakai Matuka A Wani Fada Da Suka Gwabza A Lardin Nuristan


Ma’aikatar Tsaron Afghanistan tace Sojojin kasar,da dakarun da Amurka ke yiwa jagoranci sun kashe ‘yan gwagwarmaya masu yawan gaske a wani fada da suka gwabza jiya lahadi a lardin Nuristan dake gabashin kasar.

Babu daya daga cikin rundunonin na Afghanistan,ko Amurka da ta bada adadin mayakan sa kai da suka halaka a fadan ba.Sai dai sojojin Afganistan sun bada labarin mutuwar sojan kasar daya. Sojojin sunce babu rahoton farar hula da ya jikkata.

Amma jami’an lardin Nuristan sun musanta haka,domin acewarsu farar hula ashirin ne aka kashe, da dama kuma suka jikkata. Jami’an Ma’aikatar tsaron Afghanistan sunce an kama mayakan sakai takwas,su kuma shugabannin lardin Nuristan sunce wadanda aka Kaman duka farar hula ne.

Ma’aikatar Tsaron Afghanistan tace na binciken lamarin.

XS
SM
MD
LG