Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Jirgin Ruwa Dake Dakon Mai Da Aka Sace Ya Kusa Isa Gabar Ruwan Somalia


Makeken Jirgin Dakon Mai na Saudiyya dauke da Mai da kudinsa ya kama dala miliyan dari,da aka sace ya kusa isa gabar ruwan tekun Somaliya.

Mai Jirgin ruwan da aka sace'Sirius Star', yace babu daya daga cikin ma'aikatan jirgin su- ashirin da biyar da aka jikkata. Asabar ce 'Yan fashin jirgin ruwa daga Somalia cikin kananan jirage masu dan Karen gudu suka kama makeken jirgin ruwan dake nisan kilomita 800 daga gabar Kenya,nesa daga inda barayin suka saba yiwa jiragen kwanton bauna.

Shugaban hafsan hafsoshin Amurka Admiral Mullen, yace ya yi mamakin irin nisan gudun da 'yan fashin jirgin ruwan suke kaiwa wajen aika aikarda suke yi. Jirgin wadda Tankin Mai ne yana dauke da gangar mai milyan biyu,kuma an sace shi duk da kasancewar hadin gwiwar jiragen yaki na kasa da kasa a ruwayen Somalia domin hana irin wannan fashin.Jiragen yakin sun hada da na kungiyar Tsaro Ta NATO da kuma na mayakan ruwan Amurka.

Ministan harkokin wajen Saudiyya Yerima Saud al-Faisal,yau Talata, yace fashin abin bakin cikine. Yace fashi cikin ruwa tamkar ta'addanci ne,ya kira shi cuta wacce tilas kowa ya yake ta.

XS
SM
MD
LG