Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiyarda Gwamnatin Sudan Ta Kafa Tana Kira Da Tsagaiata Wuta A Fafatawarda Akeyi A Yankin Darfur


Wata sabuwar ƙungiyar wanzar da zaman lafiya kan yankin Darfur na ƙasar sudan ta yi kira da a daina musayar wuta a yankin, a kuma saki dukan fursunonin siyasa, yayin da ake shirin babban taron wanzar da zaman lafiya a Qatar.

Wata ƙungiya da ake kira Dandalin jama’a wadda ta ƙunshi ministoci da kuma shugabannin ƙungiyoyin adawa ce ta sanar da waɗannan shawarwarin yau. Dandalin ya kuma yi kira da a ƙirƙiro da sabon muƙamin mataimakin shugaban ƙasa na yankin Darfur. Shugaba Omar-al-Bashir zai sanar da waɗannan shawarwari gobe Laraba.

Mr. Bashir ne ya kafa wannan dandalin ’yan makonni da suka shige bayanda babban mai shigar da ƙara na kotun sauraron ƙararrakin ƙasa da ƙasa suka yi kira da a tuhume shi da aikata laifufukan yaƙi dangane da rikicin yankin Darfur da aka shafe shekaru shida ana fama da shi.

XS
SM
MD
LG