Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Sake Aza Dokar Hana Fita A Birnin Omdurman bayan hari da Yantawaye suka Kai Khartoum A Karshen Mako


Gwamantin Sudan ta sake kafa dokar hana fita a birnin Omdurman,kwana biyu bayan ‘yan tawaye daga Darfur suka kai hari kan fadar kasar.

Ma’aikatar cikin gida ta fada yau litinin cewa,Jami’an tsaro har yanzu suna farautar mayakan daga kungiyar tsaida adalci da daidaituwa ko JEM.Shugaban kungiyar Khalil Ibrahim, ya gayawa manema labaru ta woyar tarho a yau cewa har yanzu yana Omdurman.Ibrahim yace ‘yantawayen zasu kaddamar da karin hare hare da nufin kifar da gwamnatin kasar.

Gwamnatin Sudan tana tayin bada goron milyan dari da ashirin ga duk wadda zai bata labarin da zai kai ga kamun Ibrahim.’

Yantawayen sun kai hari kan fadar kasar ranar Asabar bayan ratsa Sudan,tafiyar darururwan kilmotoci daga Darfur.

Shugaban Sudan Omar al-Bashir yace mayakan sa sun hana harin samun nasara.

XS
SM
MD
LG