Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Tana Neman Tarayyar Turai Ta biya Ta Diyya


Sudan ta bukaci Tarayyar Turai ta biya diyyar dala dubu arba’in ga iyalan makiyaya hudu da suka mutu lokacin da suke kokarin daukar gawar sojan Faransan nan dake aikin kiyaye zaman lafiya, kusa da kan iyakar Sudan da Cadi cikin makon jiya.

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Sudan, Ali al-Sadiq, yace al’adace a Sudan, a biya dangin wanda aka kashe ba bisa ganganci ba. A yau litinin, yace kima kan duk mutum guda da ya mutu shine dala dubu 10.

Rundunar sojojin Sudan tace makiyayan hudu sun mutune sakamakon tashin gurnetin sojan da ya mutu,lokacinda suke kokarin dora gawarsa kan rakumi.

XS
SM
MD
LG