Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'adda Sun Kai Hari A India,Har sun Kashe Mutane Da Dama.


’Yan sandan Indiya su na kyautata zaton cewa ’yan ta’adda ne suka kai wasu hare-hare da maraicen yau larabar nan a birnin Mumbai a kudancin kasar.

Kafofin labarai a birnin sun ce mahara dauke da manyan bindigogi da gurneti sun kai farmaki a kan wasu wurare hudu, ciki har da hotel-hotel biyu da tasoshi biyu na jiragen kasa, inda suka kashe mutane da dama.

’Yan sanda sun ce a yanzu haka, maharan sun killace kansu a daya daga cikin hotel-hotel din.

XS
SM
MD
LG