Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitaccen Tarihin Dan Takararar Shugabancin Amurka Na Jam'iyyar Republican,Senata John Mccain.


An haifi John McCain a yankin Panama canal,a shekarar 1936.

Mahaifinsa da kakansa dukkansu sun riki mukaman Janar a rundunar sojan ruwan Amurka. Wannan ya taimaka wajen shigar McCain Kolejinhoras da kananan hafsoshin ruwa. Bayan ya kammala horo,aka daukeshi aiki a matsayin matukin Jirgin-Saman Yaki,inda daga bisani aka turashi yakin Vietnam.

A wannan yakin ne aka harbo jirginsa a Arewacin Vietnam, a shekarar 1967,inda aka kamashi a matsayin fursinan yaki. Babu irin duka da sauran nau'in azaba da ba a gana masa ba lokacinda yake tsare. Sai da yayi shekaru biyar yana hanu kamin a sako shi. Ya dawo gida a mtsayin gwarzon namiji maikishin kasa.

McCain yace fadi tashinsa na yaki,shi ya bashi kawarer da ake nema ga masu neman shugabancin Amurka. A tsawon wa'adi hudu da John McCain yayi yana dan Majalisar dattawan Amurka mai wakiltar Jihar Arizona,ya shahara a matsayin wani gwani a fagen harkokin waje,tsaro,da ma siyasar cikin gida,har ta kai na maa kirarin "gwanin gwanaye".

A shekara ta 2000,McCain ya gwada takarar shugabancin Amurka,inda Gwamnan Jihar Texas a wancan lokaci,kuma shugaban kasa na yanzu,George Bush, ya kadashi a zaben fidda gwani na Jam'iyyarsu ta Republican.

McCain yana fatan samun goyon bayan 'yan Jam'iyyarsa ta Republican,da masu kada kuri'a da basa goyon baya wata Jam'iyya ('Yan Indipenda), a wannan karo na biyu da yake takara,inda ya maida karfin yakin neman zabensa kan batun tsaron kasa.XS
SM
MD
LG