Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Isra'ila da Na Falasdinawa Sun Cimma Yarjejeniya


Jami'an Amurka sun ce shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas, da firayim ministan bani Isra'ila Ehud Olmert, da kuma shugaba George Bush na Amurka zasu gana yau laraba a Washington.

Tattaunawar da zasu yi zata zo kwana guda a bayan da 'yan bani Isra'ila da Falasdinawa suka yarda su koma kan teburin shawarwarin neman zaman lafiya ba tare da jinkiri ba.

A cikin wata sanarwar da suka bayar a wajen taron zaman lafiya na gabas ta tsakiya da ake yi a birnin Annapolis, Mr. Olmert da Mr. Abbas sun ce gwamnatocinsu zasu sake farfado da shawarwarin neman zaman lafiya da aka jima da dakatarwa, a wani yunkurin cimma yarjejeniyar da zata kai ga kafa kasar Falasdinu a gefen Isra'ila nan da karshen 2008.

Shugaba Bush ne ya karanta jawabin hadin guiwar shugabannin biyu, inda a ciki gwamnatocin biyu suka bayyana kudurinsu na kawo karshen zub da jinin da aka shafe shekara da shekaru ana yi, tare da wanzar da sabon babi na zaman lafiya. Sanarwar ta ce Mr. Olmert da Mr. Abbas zasu ringa ganawa mako bibbiyu, yayin da wani tsayayyen kwamiti na aiwatar da shirin nasu zai gana ranar 12 ga watan Disamba.

A lokacin da yake jawabi a wajen taron, Mr. Olmert ya ce shawarwarin da za a yi zai shafi dukkan batutuwan da ba a warware su ba. Shi kuma Abbas ya bukaci al'ummar Falasdinawa da su zauna cikin kwarin guiwar cewa zasu samu kasarsu 'yantacciya.

A karshen zaman taron jiya talata, sakatariyar harkokin wajen Amurka, Comdoleeza Rice, ta ce taron kolin na Annapolis, harsashi ne ba wai karshen hanya a kokarin cimma zaman lafiya ba.

XS
SM
MD
LG