Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan ZAnga Zanga A Thailand Sun Hana Jiragen-sama Tashi.


Masu zanga zangar ƙin jinin gwamnati a Thailand sun yi tururuwa zuwa babbar tashar sufurin jiragen sama ta ƙasa da ƙasa suka tilasta hukumar sufurin jiragen sama dakatar da zirga zirgar jirage.

Jami’an sabuwar tashar jiragen saman Thailand ta ƙasa da ƙasa Suvar-nab-humi, sun ce ɗaruruwan masu zanga zanga sun ƙetare shingayen tsayuwar ’yan sanda suka kutsa zuwa harabar tsayuwar fasinjoji bayanda hukuma ta yi ƙoƙarin tattaunawa da su. Wakilan ƙungiyar rajin Damokaraɗiya sun ce burinsu shine ganin an rufe tashar jiragen saman har sai PM Sonchai Wongsawat ya yi murabus.

Mamaye tashar jiragen saman ya biyo bayan wata arangama mai zafi da aka yi yau inda masu zanga zangar ƙin jinin gwamnati suka fatattaki magoya bayan gwamnati a kan wani babban titi dake Bankok babban birnin ƙasar. Aƙalla mutane biyar ne suka jikkata.

XS
SM
MD
LG