Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senata Hillary Clinton Ce Obama Zai Zaba Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka?


Kafofin labarun Amurka na ci gaba da yayata cewar akwai sunan ’yar Majalisar Dattawan Amurka Hillary Clinton a jerin sunayen waɗanda shugaban Amurka mai jiran gado Barack Obama ke son ɗaukan guda domin riƙe matsayin sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ma‘aikatar da ita ce ta biyu a muhimmanci bayan ma’aikatar tsaron Amurka.

An sami rahoton ganin Barack Obama tare da Hillary Clinton na tintiɓar juna a birnin Chicago. Sai dai a wani taron da aka gayyace ta yin jawabi yau Juma’a a mazaɓarta ta New York, Hillary Clinton taƙi cewa uffan game da raɗe-raɗin da ake yi bata matsayin sakatariyar harkokin wajen Amurka.

XS
SM
MD
LG