Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsagerun Matasan Niger Delta Sunki Dadin Azanci


Rundunar ‘yan sandan Najeriya tace har yanzu dai bata kai ga gano wadanda suka sace Sinawa biyar a yankin Niger Delta, mai fama da rigingimu ba. Shugaba Olusegun Obasanjo ya baiwa jakadan China a Najeriya tabbacin cewa shi da kansa zai dauki dawainiyar ganin cewa an sako mutanen cikin kankanen lokaci.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Rivers, Felix Ogbaudu ya gaya wa Muryar Amurka cewa har yanzu hakansu bai cimma ruwa ba, duk kuwa da kokarin da sukai tayi na gano wadannan mutane. Ya kuma musanta bayanan da ake yi cewa wadanda suka sace mutanen sun nemi a basu kudin fansa.

Gwamnatin Najeriya tace a bara kawai, tayi hasarar sama da dalar Amurka miliyan dubu hudu, sakamakon irin wadannan tashe-tashen hankula da ake fama dasu, da kuma hare-haren da ake baiwa masna’antun mai a yankin. An dai tura dubban sojoji da rundunonin kwantar da tarzoma na musamman wannan yanki, domin su kawo karshen irin wannan tsageranci. Ogbaudu yace an sanya dukkan jami’an tsaro dake wajen a cikin shirin ko ta kwana.

An dai sace mutane da dama, aka kuma kashe dimbin dakaru a shekarar da ta gabata ta 2006, a yankin Niger Delta. A halin yanzu tsagerun, masu dauke da makamai suna rike da ‘yan kasashen waje tara, cikinsu har da sinawan guda biyar. Nageriya ita ce tafi ko wacce kasa a Afrika fataucin man fetur, wanda ke samar da kashi 95 bisa dari na kudadenta na shiga.

XS
SM
MD
LG