Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsagerun Niger Delta Sun Sake Sace Mutane


Wadannan ‘yan bindiga sun sace fiye da mutum dari, a cikin shekara daya. An riga an saki yawancinsu.

Idan aka hada da wadannan mutum ukun na karshe, a halin yanzu akwai ‘yan kasar waje kimanin takwas kenan da har yanzu suke hannu. Tsageru daga kudancin Najeriya sun jima suna sace mutane, suna kuma kai hare hare kan ma’aikatun man fetur, domin su tilasta samun bakin magana kan miliyoyin nairorin da ake samu daga albarkatun man fetur na yankinsu.

Najeriya ita ce kasa mafi arzikin manfetur a Africa. Tana hako ganga miliyan biyu da dubu dari shida na man fetur a kullum. Amma matsalolin tsagerun nan, sun jawo ragin abin da ake hakowa a halin yanzu, da kusan kashi daya bisa hudu.

XS
SM
MD
LG