Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsagrun Najeriya Sun Saki Jaririyar Da Suka Sace: Na Nijar Sun Koyi Saka A Mugun Zare


Jami’an Gwamnatin najeriya a birnin Fatakwal sunce yarinyar na cikin koshin lafiya, kuma ba a bayar da ko kwabo a matsayin kudin fansa ba.

Ministan harkokin Wajen Birtaniya, David Miliband ya gode wa hukumomin Najeriya saboda namijin kokarin da suka yi wajen ganin yarinyar ta koma hannun iyayenta lami lafiya.

Mahaifiyar yarinyar, Oluchi Hill, wacce ‘yar asalin najeriya ce, tace da fari ‘yan bindigar sun tuntubi iyalinsu, suna barazanar kashe yarinyar, daga nan kuma sai suka nemi a biyasu wadansu kudi da ba ta baiyana ko nawa ne ba.

Oluchi Hill ta shaidawa wani dan jarida cewa da alamu ‘yar tata na cikin koshin lafiya, amma kuma akwai alamun cizon sauro a jikinta. A jiya Lahadi ta kai yarinyar wani asibiti domin a duba lafiyarta.

A wani labarin makamancin wannan, jami’an diplomasiyyar kasar Sin ko kuma China, sunce wani dan kasuwar kasarsu da aka kame a Jamhuriyar Nijar, baya cikin wani hadari.

Jaridar China Daily ta jiyo daga Ofishin Jakadancin China a Jamhuriyar Nijar, cewa ‘yan tawaye suna ruke da mutumin, amma rayuwarsa bata cikin hadari. Ance mutumin da ‘yan tawayen suka sace, babban manaja ne a wani Kamfanin Sarrafa Ma’adinain Atom na China, wanda ke aikin hakar ma’adinin uranium a Kasar ta Nijar.

Wata kungiyar Buzaye mai da’awar neman tabbatar da adalci ga al’ummar Nijar, ta dauki nauyin wannan ta’asa.

XS
SM
MD
LG