Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaba Fujimori na Peru Ya Gamu Da Gamonsa


Kotun Kolin kasar Peru, ta yankewa tsohon Shugaban Kasar Alberto Fujimori hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari, saboda bada umarnin ayi wani haramtaccen bincike.

Ranar Talata, Alkalin Kotun Koli Pedro Urbina ya sami Fujimori da laifin bada umarnin a ayi bincike ba tare da takardar izini ba, a gidan uwargidan tsohon babban jami’in tsaro, Vladmiro Montesinos.

Tsohon Shugaban na Peru, yace hakika ya bayar da umarnin ayi wannan bincike, amma yayi hakan ne saboda a tantance zargin halatta kudin haram da ake yiwa Montesinos.

Ranar Litinin aka gurfanar da Fujimori kan wadansu zarge zargen na dabam, na kashe ‘yan tawaye masu akidar gurguzu, lokacin da yake shugabancin kasar. Zai iya fuskantar daurin shekaru 30 idan aka tabbatar da wannan laifi a kansa.

A lokacin da yake kare kansa, Tsohon Shugaban ya hasala, inda ya rika wadansu kalamai cikin fushi, har saida daya daga cikin alkalan kotun ya taka masa burki. A yau laraba ake sa ran ci gaba da shari’ar.

XS
SM
MD
LG