Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Saura Kwana Hudu Ayi Zaben  Shugaban Kasar Amurka 'Yan Takara Sun Zafafa Yakin Neman Zabe.


‘Yan takarar shugaban Amurka biyu John McCain da Barack Obama yau Juma’a sun duƙufa ka’in da na’in wajen ci gaba da gangamin yaƙin neman zaɓensu inda suke ƙarfafa bayani kan yadda za’a farfaɗo da tasirin tattalin arzikin Amurka dasamarwa Amerkawa ayyukan yi.

Jami‘an yaƙin neman zaɓen Barack Obama na jam’iyyar Democrat sun banzama zuwa Iowa-tsakiyar yammacin Amurka, amma sun shirya fara yada zango a Indiana, jihar da jam’iyyar Republican keda ƙarfin gaske a zaɓukan baya, amma yanzu ƙididdigar ra’ayin masu jefa ƙuri’a ta nuna Obama ne a sahun gaban McCain a jihar.

Shi kuma Ɗan takarar jam’iyyar Republican John McCain ya doshi jihar California bayan ya yada zango a Ohio. A can California ɗin zai yi jawabin haɗin gwiwa tare da gwamnan jihar mai farin jini Arnold Schwarzenegger.

Masu fashin baƙin siyasar Amurka sun jaddada cewar ba wanda zai iya samun nasarar zama shugaban Amurka ba tare da ya sami amincewar masu kaɗa ƙuri‘ar jihar Ohio ba.

XS
SM
MD
LG