Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Mai Jiran Gado,Obama,Ya Nada Sabon Kwamiti Da Zai Bashi Shawara Kan Tattalin Arziki.


Shugaban Amurka mai jiran gado Barack Obama,ya nada tsohon shugaban babban Bankin Amurka Paul Volcker, ya shugabanci wani sabon kwamiti da zai bashi shawara kan hanyoyin farfado da tattalin arzikin Amurka dake fama da matsaloli.

Mr.Obama yace sabon kwamitin bada shawarwari kan hanyoyin farfado da tattalin arzikin zai yi aiki shigen kwamitinda ba ya la'akari da siyasa wajen baiwa shugaban kasa shawarwari gameda harkokin tsaro.

A yau laraba Mr. Obama ya bada sanarwar nadin, a taron manema labaru a birnin Chicago.

Mr. Volcker ya taba rikon mukamin shugaban babban Bankin Amurka daga 1979-87. Kuma yana daya daga cikin manyan masu baiwa Obama shawara lokacinda yake yakin neman zabe.

Ahalin yanzu kuma, Shugaban Amurka mai jiran gado Barack Obama,yace ya kamata a bana shugabannin Bankunan Amurka, su hana kansu karbar tukuicin karshen shekara na miliyoyin dala da ake basu, domin su nuna nadamar matsalar tattalin arziki da suka shigarda Amurka ciki ahalin yanzu.

A wani bangare na hirarsa da tashar talabijin ta ABC wadda za a nuna yau laraba da maraice,Mr.Obama yace ya kamata shugabannin kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Amurka(watau Wall Street) su gane cewa Amurkawa suna fama cikin wannan mawuyacin hali.

Yace shugabanni da tuni suka mallaki tulin miliyoyin dala, tilas su nuna sadaukadda kai, yana mai cewa abu mafi kankanci da zasu iya nunawa ke nan. Haka kuma Mr. Obama ya zargi shugabannin kamfanonin kera motoci wadanda suka zo Washington cikin jirage mallakar kamfanonin, domin neman Majalisar dokoki ta tallafa musu da rancen kudin Talakawa domin ceto kamfanonin dake neman durkushewa.

Shugaban mai jiran gado, yace shugabannin manyan kamfanonin kera motocin, kusan basu san abinda yake faruwa cikin kasar nan ba.

XS
SM
MD
LG