Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wato Kotu Ta Sami Wani Sojan Amurka Da Laifin Kisan Awwad


A ranar Laraba ayarin masu yanke hukunci a garin Camp Pendleton, a jihar California, Suka sami Kofur Trent Thomas da hannu a kisan Hashim Ibrahim Awwad, dan shekaru 52, a garin Hamdania.

Amma dai sun wanke shi daga zargin shirya kisan, yin bayanan karya da kuma fasa gida.

Thomas yana daya daga cikin sojojin Ruwan Amurka bakwai da wani likitansu da aka gurfanar gaban kotu dangane da wannan kisa na watan Aprilun 2006.

Sojojin sunce shugabansu ne ya umarce su da su kamo wani da ake zargin dan gwagwarmaya ne, kuma su kashe shi, amma da basu sami mutumin a gidansa ba, sai kawai suka shiga gidan Makwabcinsa Awwad, suka hallaka shi a madadi.

XS
SM
MD
LG