Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Kunan Bakin Wake Sun Sake Barna A Iraq


Hukumomin Iraq sunce wani dan kunan bakin wake ya kashe mutum goma sha hudu a Arewacin Iraq, cikinsu har da sojojin Amurka guda biyu.

‘Yan sanda da Sojojin Amurka sunce a kalla wasu mutum goma sun sami raunuka, lokacin da dan kunan bakin waken ya tashi bom a cikin taron jama’a, kusa da wani shingen binciken tsaro dake garin Kanaan, a lardin Diyala jiya Alhamis.

‘Yan sanda sunce bisa dukkan alamu, an nufi wadansu larabawa ‘yan Ahlul Sunnan ne da wannan hari, wadanda suka shiga sahun sojojin Amurka wajen yaki da ‘yan gwagwarmaya.

A wani labarin na dabam, Rundunar Sojin Amurka a Iraq, tace ta gano gawawwakin mutun 26, da aka binne a kusa da wani wuri da ake amfani dashi wajen azabtar da mutane, a garin

XS
SM
MD
LG