Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Kungiyar Taliban Sun Kai Hari Kan Gine Ginen Gwamnati A Kabul


Wani gagarumin hari da kungiyar Taliban ta kai akan gine ginen gwamnati da dama a birnin Kabul kasar Afghanistan ya kashe akalla mutane biyar kuma fiye da mutum saba’in sunji rauni.

Shugaban hukumar leken asirin kasar Amrullah Saleh, yace mahara guda bakwai dauke da bindigogi masu sarafa kansu, sanye kuma da falmaran harin kunar bakin wake sun kai hari ne a lokacin cunkoson safiyar litinin, al’amarin daya haddasa mummunar musayar harbe harbe tsakanin maharan da yan sanda. Yace jami’an tsaro sun kashe dukkan maharani su bakwai.

Shi dai Mr. Saleh bai ce komai ba akan rahotani dake cewa maharan sun shigo kasar ne daga Pakistan. Jami’ai sunce maharan sunyi shirin mamaye muhimman ma’aikatun gwamnati sa’anan su kutsa fadar shugaba, to amma basu sami nasara ba.

Bayan harin ne shugaba Hamid Karzai ya gabatar da sanarwa yana mai fadin cewa birnin na hannun gwamnati daram. Jami’ai sun baiyana cewa shugaba Karzai yana rantsar da sababbin wakilan Majalisar ministocinsa a lokacinda tarzomar ta barke.

XS
SM
MD
LG