Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Takarar Shugabancin Amurka Sun Koma Dagar Yakin Neman Zabe


‘Yan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam’iyyun siyasa biyu John McCain na Republican da Barack Obama na Democrat sun koma filin dagar yaƙin neman zaɓe ana sauran makonni biyu aje rumfunan zaɓen shugaban ƙasa.

An shirya cewar Senata McCain zai yi jawabin gangamin zaɓensa a Miami da Melbourne jihar Florida, shi kuma Senata Obama zai yi nasa gangamin yaƙin neman zaɓe a Virginia da Missouri.

‘Yan takarar biyu sun haɗu da juna a daren jiya Alhamis a wajen bikin cin abincin dare domin gangamin neman gudummawar agajin da aka saba yi kowace shekara don tallafawa masu buƙata da sunan tsohon Gwamnan New York Al-Smith wanda yayi nasa gangamin yaƙin neman zaɓen a shekarar 1928 amma bai sami nasara ba.

XS
SM
MD
LG