Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takara Sun Shiga Makon Karshe na Yakin Neman Zabe


Ana sauran mako daya kacal kafin babban zaben shugaban kasar da za'ayi a nan Amurka, 'yan takarar shugaban kasar suna ta kai da kawo, kowanne na kokarin cusawa Amurkawa ra'ayin cewa shine zai fi kuzarin gyara tabarbarewar tattalin arziki da kuma chanja yadda ake gudanarda harakokin mulki a Washington.

Kuma duka 'yan takaran biyu, Barack Obama na Democrats da John Mccain na Republicans suna waye garin wannan safiyar ta Talata ne a jiha daya ta Pennsylvania kafin su zarce zuwa sauran jihohin da suke kat da kat da juna a wajen tagomashin jama'a.

Duk da cewa duk ra'ayon jama'a na nuna cewa shine a gaba wajen tagomashi, Barack Obama na ci gaba da gayawa magoya bayansa cewa su manta da wannan, suje suci gaba da zare dantsen yaki gadangadan, ba kakkautawa:Mukarraban Obama sunce zai gabatarda abinda suka kira "hujjojinsa na karshe" a wannan kyamfen, inda zaici gaba da nuna cewa zabar John McCain, kamar ci gaba da zama karkashin mulkin shugaba Geroge Bush ne.

A nasa gefen, John McCain, wanda Obama ya baiwa tazarar maki bakwai a wurin tagomashin jama'a, yana ci gaba da gayawa nashi magoya bayan cewa in sun zabi Obama, zai dirka musu haraji, kuma ya maida Amurka karkashin tsari irin na 'yan gurguzu:

A halin yanzu kuma…hukumomi a jihar tennesee sun cafke wasu mutane biyu da akace suna kulla makarkashiyar kashe bakaken fatar Amurka – ciki harda Barack Obama. An tuhumci wadanan mutanen biyu da laifin mallakar makamai, kulla makircin satar bindigogi da kuma yin barazana akan rayuwar wani dan takaran shugaban kasa.

Hukumomi sunce koda aka cafke wadanan mutanen biyu a ranar Larabar da ta gabata, suna tareda bindigogi, suna kuma shirin yin fashi akan wani kantin saida makamai.

XS
SM
MD
LG