Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yansandan Pakistan sun kama tsohon zakaran kwallon Cricket,Imran Khan


‘Yansandan Pakistan sun kama Imran Khan, tsohon zakaran kwallon Cricket, da ya zama dan siyasa a kasar, bayan ya fita bainin jamaa a karo na farko tun lokacinda Gwamnatin kasar ta kafa dokar ta baci.

Khan ya fito daga inda ya buya domin yayi jawabi ga taron dalibai yau Laraba, a Jami’ar Punjab dake birnin Lahore, a gabashin kasar. Jim kadan da isar sa harabar jami’ar, sai aka kamashi.

An tuhumeshi karkashin dokar kasar ta yaki da ta’addanci,wacce ta tanadi hukuncin kisa ko daurin rai da rai.

Tsohuwar Pime Minista, kuma jagorar adawa Benazir Bhutto, har yanzu tana karkashin dokar talala a gidanta dake Lahore.

Kakaki Sherry Rehman, ta Jam’iyyar PPP, ta Ms Bhutto, tana zantawa da sauran yan sisaya dake adawa da nufin hada karfi wuri guda domin yaki da dokar tabaci da kuma shugaba Pervez Musharraf.

Tsohon PM dake gudun hijira, Nawaz Sherriff, yace a shirye yake yayi aiki da Ms. Bhutto. A hira da yayi da Muryar Amurka da ake kira Deewa Radiyo, Mr.Sherrif yace yana da wuya yan adawa su hada karfi wuri guda ganin shugabannin su duka suna hanu.

Ita kuma Gwamnatin shugaba Bush ta sake nanata kira da tayiwa Pakistan cewa ta janye dokar ta baci da ta kafa, kuma ta kaddamarda zabe sahihi,duk ci gaba da tirjewar shugaba Pervez Musharraf.

Kakakin fadar White House, Dana Perino, a yau Laraba, tace yana da wuya a tsammaci zabe sahihi a yayinda Pakistan take karkashin dokar ta baci.

Amma shi kuma a hira da yayi da jaridar New York Times da aka buga yau Laraba,Janar Musharraf ya dage cewa an kafa dokar ta bacin ne domin tabbatar da anyi zabe sahihi. Shugaban na Pakistan yayi alkwarin kaddamarda zabe a farkon watan Janairu idan Allah ya kaimu.

XS
SM
MD
LG