Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rilwan Lukman Yana Cikin Jerin Sunayen Mutane Goma Sha Uku Da Shugaban Najeriya Ya Gabatarwa Majalisar Dattjiai Domin A Nadasu Ministoci.


Shugaban Najeriya ya gabatar da sunayen mutane da ya zaba ministoci mako uku bayan ya kori rabin wakilan Majalisar Zartawarsa a wani garambawul da aka yi dakonsa na lokaci.

A yammacin daren jiya ce Shugaba Umaru Musa 'Yaradua ya aikewa Majalisar Dattijai jerin sunayen mutane 13 da ya zaba domin basu ministoci.

Jerin sabbin sunayen sun hada da tsohon ministan Mai Rilwanu Lukman,wanda ake kyautata zaton shi za'a baiwa ministan makamashi mukamin da shugaban kasar yake rike dashi a halin yanzu. Lukman ya kuma taba zama shugaban kungiyar kasashe masu arzikin mai(OPEC).

XS
SM
MD
LG