Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraq Ta Yarda Amurka Taci Gaba Da Kasancewa Cikin Kasar Har Zuwa 2011.


Jakadan Amurka a Iraqi ya bayyana yarjejeniyar ci gaba da zaman sojin Amurka a Iraqi da sunan muhimmin abinda zai shiga tarihi.

Jakada Ryan Crocker ya furta hakan ne a wani jawabin sanya hannu a daftarin yarjejeniyar tare da ministan harkokin wajen Iraqi Hoshyar Zebari. Jakadan na Amurka yana mai jaddada cewar haƙiƙa yarjejeniyar zata ƙarfafa matakan tsaron ƙasar Iraqi tare da inganta zumunci tsakanin Amurka da Iraqi.

A jiya lahadi ce majalisar gudanarwar Iraqi ta kaɗa ƙuri‘ar amincewa aiki da yarjejeniyar wadda zata baiwa Amurka damar ci gaba da ajiye sojinta a Iraqi har zuwa ƙarshen shekarar 2011.

XS
SM
MD
LG