Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau G8 Tana Tattauna Bashi da Talauci A Afirka


Shugabannin Manyan kasashen Duniya masu Arzikin Masna’antu, zasu sadaukar da yau juma’a, wacce ita ce ranar karshe ta taron da suke yi a Jamus, ga batutuwan yafe bashi da yakar talauci a Africa.

Mai masaukin taron, kuma Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Markel tana rokon a sami karin alkawuran agaji ga kasashen Africa.

Shugaba Bush ya sanarda agajin dala miliyan dubu talatin daga Amurka, don samarda magungunan cutar AIDS a Africa.

Prime Ministan Birtaniya Tony Blair ya jaddada bukatar bin sawun alkawuran da kasashen suka yi a taronsu na Birnin Gleneagles, na Kasar Scotland, shekaru biyu da suka wuce.

Saidai wadansu masu rajin taimakawa Africa sunce sabunta alkawura kawai ba zai wadatar ba a halin da ake ciki.

XS
SM
MD
LG