Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Sugaban Najeriya Ke Fara Ziyarar Aiki A Amurka


Shugaba Umar Musa ‘Yar Aduwa Na Najriya sauka a Birnin Washington D.C., domin fara wata ziyarar aiki ta kwana biyu. Da misalin karfe tara na daren Laraba, (lokacin Washington) Shugaban ya sauka tare da Uwargidansa Turai da sauran manyan mukarraban gwamnatinsa.

Da safiyar Alhamis Shugaba ‘Yar Aduwa zai gana da Shugaba Bush na Amurka. Da yamma kuma zai jagoranci tattaunawa tsakanin ‘yan kasuwar Amurka da na Najeriya, daga nan kuma ya zarce Ofishin Jakadancin Najeriya a Amurka, inda aka shirya masa liyafa.

Da safiyar Juma’a kuma zai tashi zuwa birnin New York, inda zasu ci gaba da tattauna batun zuba jarin Amurkawa a Najeriya, kafin ya koma gida Najeriya.

Najeriya babbar abokiyar cinikin Amurka ce,inda take kasa ta biyu da tafi sayarwa da Amurka man fetur.

XS
SM
MD
LG