Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Iya Gurfanar Da Kamfanonin Da Suka Taimakawa Wariyar Al’umma A Gaban Kotunan Amurka


Wata kotun daukaka kara a nan Amurka ta bayar da dama a gurfanar da wasu kamfanoni a gaban kotu, asboda zarginsu da ake yi da tallafawa akidar wariyar al’umma a Africa ta Kudu.

Kotun wacce tayi zamanta a birnin New York, tace wani alkalin Kotun Manhattan ta New York din, ya tafka kuskure a lokacin da ya kori wannan kara a shekara ta 2004.

Masu gabatar da kara a shari’ar, sunce kamfanonin sun hada baki da gwamnatin Africa ta Kudu, wajen tabbatar da tsarin wariyar launin fata.

Gwamnatin Amurka tana adawa da wannan kara, inda tace ci gaba da ita zai iya kawo cikas ga kokarin da ake yi na sulhunta tsakanin mutanen Africa ta Kudu, zai kuma iya raunana dangantaka tsakanin Africa ta Kudu da Amurka.

Ita kanta Africa ta Kudu tace bata kaunar wannan shari’a, inda tace wannan ya saba wa damarta ta tabbatar da adalci ga mutanen kasarta, yadda ta ga ya dace.

A shekarar 1994 aka kawo shen mulkin wariyar al’umma a Africa ta Kudu, lokacin da kasar ta gudanar da zaben da ya a karon farko ya hade al’ummar kasar, Nelson Mandela kuma ya zama Shugaban kasa na farko a wannan tsari.

XS
SM
MD
LG